GYARA MUKE
Salam! Fans na Nectar Boy masu hawa Okadabooks, ina so in sanar daku cewa muna wani gyara akan okadabooks. Domin muna so mu kara sa tsaro a littatafanmu daga barayi masu sato labaran mu suna turawa a whatsapp da facebook, wasu ma har suna saka lambobin wayarsu akan wai a neme su ta whatsapp su suke yin rubutun books. A dalilin haka mun boye littatafan har sai mun kammala gyaran da ake yi. Sai ku dan kara hakuri kadan. Yanzu in kuka hau okadabooks zaku ga babu littatafan mun boye su. Kamar yanda na maku wannan sakon na bada hakuri akan cewa mun dakatar dasu haka zan maku sakon albishir cewa mun maido su kowa ya cigaba da harka. zalan dawo maku da sabbin littatafai irinsu 'MATAR YAYA 2017' karashen YAWON DUNIYA, TSINTACIYAR MAGE da sauransu. Daga naku a kullum NECTAR BOY.