Posts

Showing posts from June 17, 2018

GIDAN MALAM

GIDAN MALAM ••••••••••••••••••••• Ni dai sunana Rattaba'una Sammani, amma saboda wahalar ambaton sunan, sai mutane suke kira na Ba'una, a lokacin ban damu ba, ina amsawa tunda dai suna na ne, kamar wasa sai aka fara kira na Bauna, sunan wata dabbar daji, tun ina maishe da abun wasa, naga fa da gaske har manyan mutane haka suke kirana, sai na fara fada ina zagi akan cewa bana son sunan. In an kira ni Bauna sai ince wa mutum Baban ka ne Bauna, ko ince buge masa gwailaye, watarana ma har dutse nake jifar mutane dashi in aka kira ni wanga suna.  Ba sai na zama abun tsokana ba a kauyen mu, kowa ka gani babba da yaro sai a kira ni da Bauna, sai in rarumi duwatsu su kuma su zuba a guje ina jifa da zage zage. Wai fa duka shekaruna basu wuce goma sha uku ba a duniya lokacin nan. Hakanan aka maishe ni mahaukacin karfi da yaji. Idan na gaji da jifan mutane sai in koma gidan mu wajen Mama ina kuka. Haka zata rungume ni tana lallashi tare da ban hakuri akan cewa in daina