YAWON DUNIYA (episode 8)
YAWON DUNIYA (episode 8) ••••••••••••••••••• Cigaban labarin Nectar Boy wato YAWON DUNIYA. Idan baku manta ba, mun tsaya a inda... Na fito ina tafiyar rangwada a dole na zama mace. Na nufi hanyar fita daga gidan, wato inda su Sadi da sarauniya suke a durkushe gaban sarki. Ina zuwa na durkusa alamar gaisuwa gaban sarki, sannan na nufi hanyar fita daga gidan. Har na kai bakin kofa sai Sarki yace, "wacece nan cikin dare, me kike anan?" Cikin muryar mata nace, "nice Sadiya yar aikin gidan nan". Sadi yace, "wallahi shine". Dogarawa sukace, "shine wa?" Sadi yace, "shine Nectar almajirana". Kafin ayi wata magana sai ga dogarawan da suka je dakina sun dauko gimbiya a zindir, sukace, "almajirin bayanan bamu ganshi ba". Sarki yace, "ku kamo shi gashi can". Haba ni da ke bakin kofa sai na jefar da mayafi, na tsala a guje ba kaya, kaciya tana tsalle ina lafta gudu. Dogarawa suka rufa min baya a guje suna sai su