Posts

Showing posts from May 7, 2017

YAWON DUNIYA (All Episodes)

Image
ADVENTURES OF NECTAR BOY YAWON DUNIYA ••••••••••••••••••••• Labarin yawon duniya na Nectar Boy a dunkule gaba daya. Labarin ya samo asali ne inda saurayin yaje wajen budurwarsa amma tayi masa wulakanci akan bai da ko sisi, ta samu mai kudi. Shine ya fusata yayi niyyar shiga duniya domin yayi arziki. Nectar Boy da babban abokinsa Sadi suka shiga duniya domin sheke ayarsu da kuma neman kudi. Sai dai sun hadu da kalubale kala-kala. Shin yaya wannan Yawon duniyar zai kasance. Duk inda suka je sai kaji sunci duri, ko dai suyi kwartanci, ko suyi yaudara da sauran su dai. Sunci addabi matan mutane a cikin duniya. To ga Complete Episodes nan daga 1-10 a dunkule cikin rahusa. Sai ka shigo daga ciki musha karatu. Uhmm! Taba ka lashe daga littafin YAWON DUNIYA..... ....... Na fito kan hanya zanje gona, sai ga Rahane tafe tana rangwada, bakinta tana taunar cingam, ga janbakin nan ta rangada yayi mata kyau gwanin sha'awa. Ina ganinta na washe baki nace, "su Rahane yanmata".