Posts

Showing posts from June 5, 2022

CIN ZUBAINA

Image
  Tunda suka bar tashar anguwa uku, basu zame ko ina ba sai gidan su Zubaina dake Lamido crescent Kano. Sambo ya hangame baki yana mamaki, ashe Zubainar da yake rainawa a waya yana tunanin wata yar qaramar karuwa ce suke batsa, ashe diyar manyan mutane ce. Yaga gidansu makeke, an zuba naira wajen kera wannan gida. Gidan an rba shi kashi hudu, ko wane sashi gida ne mai zaman kanshi, ga yan aiki suna kai komowa. Da shigar su aka bude masu qofa ana gaishe su. Anan Zubaina ke sanar da yan aiki cewa wannan danuwanta ne yazo ziyara. Nan suka qara girmama shi. Zubaina ta nufi daya daga cikin gidajen dake harabar gidan, Sambo na biye da ita a baya. Zubaina tasa mukulli ta bude kofar gidan, suka shiga ciki. A cikin falon ne Sambo yaga abinda ya ruda shi, falon ya tsaru iya tsaruwa. A bangon akwai hoton wani mutum zai kai kimanin shekaru sittin da doriya. A gefen hoton kuma ga hoton Zubaina nan, "ina tunanin wancan shine mahaifinta gaskiya Sambo ya kiyasta a zuciyar sa. Suka zauna cikin fal