CIN JANET
******** Wayyo ni Nectar! Ina zan saka kai na da wannan wahalar dake neman afko min, ni a lokacin bama tunanin Baban su Jenifa nake ba, wani madarar sanyi da ake surarowa mai tattare da iska ne ke kwamacala dani a lokacin. Sai dabara tazo min, tunda akwai wutar nepa, kawai in dinga lekawa daki daki, sai in daga labule haske ya dan shigo inga ko nan ne dakin Jenifa. Ai dai dakin su Sarah zan ga mutum biyu, dakin iyayen ma zan ga mutum biyu, na Jenifa kuwa ita kadai ce. Sai na nufi dakin farko. Ina shiga dakin naga tsarin sa irin na Jenifa, na kamo labule na daga domin in haska gadon inga waye a kwance. Sai naga dundum! Nepa sun yi tsiyar tasu, an dauke wutar lantarki. Amma dai duk duniya babu tsinannu irin yan Nepa, wai su rasa lokacin dauke wuta sai yanzu zasu min lalata. Na waiga hagu da dama, sama da kasa bana ganin komai, ko tafin hannu na bana gani. Duhu ya mamaye ko ina. Kawai na yanke hukuncin nan ne dakin Jenifa, tunda dai tsarin dakin daya ne. Sai na laluba kamar makaho