BAYANI DALLA DALLA AKAN OKADABOOKS
OKADABOOKS APPLICATION Wannan wani application ne dake aiki akan wayoyi kamar android, blackberry Q ko Z series, iphone, ipad, tablet. Ana amfani dashi wajen karanta littatafan hausa da turanci, wato novels. A cikin wannan application din ne ake samun littafan hausa na Nectar boy, wannan littatafan da kuke ganin tallar su masu motsa sha'awar nan. Kowane gajeren labari da kuke gani an yanko sa ne daga cikin littafi domin ayi talla dashi. Akwai cikakken littafi mai kunshe da cikakken labarin. Zan yi bayanin okadabooks application anan, da hanyar samunsa tare da yanda ake amfani dashi. Zan dauki tsarin android wajen yin bayanin sa, domin mafi yawanci ana amfani da wayar android. *Da farko dai ana samun application dinnan a cikin PLAYSTORE na wayar android. Idan aka shiga playstore sai a danna wajen search a rubuta sunan OKADABOOKS. Ga misali nan a hoton dake kasa, an nuna wajen search da jar kibiya (arrow) Idan aka rubuta OKADABOOKS a wajen search, aka gano application di