Posts

Showing posts from April 1, 2018

GIDAN BIKI

Image
GIDAN BIKI ••••••••••••••••••• Dahiru na zaune qofar gida yana taunar gyada mai gishiri, gardin ta na ratsa kunnuwansa yana lumshe idanu. Yaji sallamar Sale, ya zauna gefensa suka gaisa. Ana yake bashi labarin cewa yazo kwana dakinsa domin baqi sunyi yawa a can gidansu, ya bar masu dakinsa na yau. Dahiru yace "Mts! Kai Sale, wai meyasa kai baka iya zuwa bane?" Sale yace "kamar yafa, ban gane ba". Dahiru yace "kasan na dade ina baka labarin Jummai, da irin wahalar da nake ta sha dan in samu tazo dakina. Yau nayi sa'a na shawo kanta, zata zo mu kwana cin duri, kai kuma sai ga ka. Kuma kasan in ban ci ta ba yau, ban san ranar da zan qara samun amincewarta ba. Zaman nan da kaga nayi, ita nake jira". Sale yayi shiru, ya jinjina kai, yaga cewa gaskiya ko shine yayi irin wannan babban kamun na yarinya kamar Jummai, to bazai yarda wani yazo ya wargaza masa shiri ba.  Don haka yace, "to ai bakomai, sai in tafi wa

DAN AUTAN HAJIYA

DAN AUTAN HAJIYA ••••••••••••••••••••• Sallau shine dan auta a gun Hajiya Marka. Tana da ya'ya guda takwas, bakwai daga cikin su mata, sai na karshen shine namiji. To ta dauki son duniya ta dora akan Sallau dan autan ta, bata ganin laifin sa ko kadan, duk abunda ya aikata daidai ne. Kasancewar Hajiya masifaffiya ce a garin, kowa yana shakkar ta, domin da ka taro fada da Hajiya, gara ka mari dan sanda a ofishin su, anan in kana da kudi zaka tsira, fada da Hajiya kuwa.... Uhm! A zauna lafiya dai, kar a tabo ta din.  To wannan gata da Sallau ya samu ga kuma tsoron Hajiya da ake a ko ina, sai yake yin abunda yaga dama a fadin garin nan, kowa na shakkar ya taba shi. Domin taba Sallau kamar taba Hajiya ne, da ka taba Hajiya kuwa, gara akuyoyin ka su fita kiwo basu dawo ba.  To kun ji wannan shine fa Sallau dan autan Hajiya, kuma abokan ja'irancin nasa sune Tanko da Idi, suna cin albarkacin Sallau. Duk inda suka ga anyi wata yar ajiya sai sun canza mat