FARIDA DA MALAM

Har Malaman jarabawar sun raba takardun jarabawar, an fara lokacin dana isa dakin jarabawar. Nan muka gaisa dasu, sai na fara aikina, wato zagayawa ina tsaron dalibai kar suyi satar amsa. Can na hango Surayya sai raba ido take tana kallo na, muna hada ido naga tasha kunu, tana min kallon Malam ya haka'. Nayi murmushi tare da kashe mata ido, sannan cikin taku na fara nufar kujerar ta. Ina zuwa daidai kujerar Farida sahibar mafarkina, sai na dan tsaya. Yau anyi sa'a,ta dago kai muka hada ido, zai zufa take, bata rubuta komai ba. Kamar jiya. yau ma tana cizon biro. To yarinyar da bata min magana taimakon me zan mata? Kawai nayi gaba, na nuti inda nasan bazan yi aikin banza ba, inda za a bani duri in kwashi lagwada. Sun gama jarabawar yau, kowa ya bada nasa ya fita. A kofar dakin jarabawar naga Farida da Surayya tsaye. Shegiya Surayya, kamar babu abunda ya faru tsakanin mu. Haka ta rusuna, tace "Malam sannu da qoqari". Nace "yauwa Surayya. ya jarabawar? Surayya tace ...