A GIRGIZA KWANKWASO 4
Maryam ta juya ta kalli kwankwason Farida, ta ganshi makeke. Sai tace, "sunan bikin mu "A GIRGIZA KWANKWASO". RANAR YAU Maryam taci ado sosai, tana sanye da riga da siket yan kanti masu bayyana surar ta. Duk wata baiwa ta kyau da take dashi ta bayyana. Haka ma Nusaiba taci ado sosai, sun hadu, da ka gansu kaga abunda ake nufi da yanmata adon gari. Suka jera tare har bakin titi, daga nan suka yi ma juna bye-bye. Maryam ta nufi wajen samo masu DJ, ita kuma Nusaiba ta tafi kasuwa domin yi masu siyayyar kayan party. Maryam ta karaso har studio din DJ abokinta. DJ na zaune yana hada wani sabon kida mai taushi da dadin sauraro lokacin da Maryam ta shiga shagon. Ta tsaya tana sauraren sautin kidan tare da jijjiga kai cikin gamsuwa da dadin sautin. "Kai DJ wannan sauti mai dadi haka", ta fada yayin da ta karasa inda yake. DJ yace, "Ah! Hajiya Maryam ce kenan, manyan gari". Maryam tace, "Haba DJ ai kune manya bamu ba. DJ wani taimako zaka min in zan samu