CHAKWAKIYA
CHAKWAKIYA *************** Labarin wata yarinya yar makaranta kuma yar bariki mai suna Maryam. A bariki ana kiranta da Maryam Bututu A makaranta kuma ace mata Maryam Sisi Ta zubar da ciki ba iyaka, ta kwanta da maza ba iyaka, bugu da kari akwai yaudara da kwacen samari. Amma fa akwai kyau kamar ita ta kera kanta. Wajen barikinta ta afka cikin chakwakiya Domin shan labarinta sai ku karanta littafin CHAKWAKIYA. *************** KADAN DAGA CIKI *************** *********** Suna ta sauri har suka isa filin rawar nan, suna zuwa suka tarar da dalibai maza da mata an yamutse ana ta rawa. Ga rungume-rungume ana tayi. Shafe-shafe da matse-matse kuwa, babu tanbadar da ba ayi a wajen. Maryam ta zuba ihu kamar wani abu ya cije ta, kowa ya waigo domin ganin lafiya! Ita kuwa ana bata filin sai ta karkace kugu, ta dora hannu akan kwankwasonta, sannan ta fara girgiza kwankwaso da jijjiga duwaiwai. Haba sai ta kara ma wutar chasu man fetur kawai, dalibai suka zunduma ih