DAN AUTAN HAJIYA
DAN AUTAN HAJIYA •••••••••••••••••••••••••• Idi, Sallau da Tanko, sunayen abokan kenan guda uku wanda suka fitini jama'a da sace da sace a cikin gari. Da an duba aka ga babu tukunya a tsakar gida sai kuji ana tambayar yara, "shin kunga Sallau da abokan sa a unguwar nan?" Idan yara suka ce, "eh ai an ga wucewar su dazu." Sai kuji matar gida tana zuba salati, ta san shikenan tukunyar ta tana kasuwa, ko kuma akuyar mutane. Haka dai duk abunda zai kawo taro da sisi a kasuwa, sai dai idan su Sallau basu dora ido akan sa ba, amma sai sun dauka. Watarana mahaifin Tanko ya kira malamin garin, aka zaunar dasu aka yi masu fada da wa'azi sosai mai ratsa jiki. Da aka gama wa'azance su, sai suka yi godiya suka fita waje. Suna fitowa Sallau ya kalla Idi suka kece da dariya. Idi yace, "wai har mu wancan me gemun can zai ma wa'azi, to bai san cewa a islamiyyar ma sai da muka yi sauka ba sannan muka fito, ni fa izu tamani