DAKIN USTAZAI
DAKIN USTAZAI ••••••••••••••• "Wayyo na shiga uku!" Basma ta fada tare da jingina da bangon hostel din. Wasu hawaye masu dumi suka kwaranyo kan fuskar ta. Ta cigaba da cewa, "Yanzu ya zan yi kenan, banda kowa a garin nan Malama a taimaka min da daki, ko mu goma ne zan iya zama. Malama Zainab me bada dakin hostel na mata tace, "Sai dai fa kiyi hakuri, kin makara. Babu dakin daya rage na haya duk jami'ar nan. Sai dai kawai ki koma cikin gari in kina da yan'uwa ki zauna dasu wannan shekarar." Basma ta fashe da kuka tace, "na rantse maki Malama banda kowa. Daga Taraba state nake, banda kowa a garin Sokoto, ko kawaye ban dasu anan balle yan'uwa." Malama Zainab taji tausayin Basma sosai. Tace, "akwai inda zan iya kwatanta maki suna bada hayar daki a kusa da nan. Bayan makaranta gidan hayar yake. Amma naga kamar bai kamace ki bane dan naga alamun ks ustaziya ce. Gidan a hade yake maza da mata." Basma tace, &q