DAKIN USTAZAI




DAKIN USTAZAI
•••••••••••••••

"Wayyo na shiga uku!" Basma ta fada tare da jingina da bangon hostel din. Wasu hawaye masu dumi suka kwaranyo kan fuskar ta. Ta cigaba da cewa, "Yanzu ya zan yi kenan, banda kowa a garin nan Malama a taimaka min da daki, ko mu goma ne zan iya zama.

Malama Zainab me bada dakin hostel na mata tace, "Sai dai fa kiyi hakuri, kin makara. Babu dakin daya rage na haya duk jami'ar nan. Sai dai kawai ki koma cikin gari in kina da yan'uwa ki zauna dasu wannan shekarar."

Basma ta fashe da kuka tace, "na rantse maki Malama banda kowa. Daga Taraba state nake, banda kowa a garin Sokoto, ko kawaye ban dasu anan balle yan'uwa."

Malama Zainab taji tausayin Basma sosai. Tace, "akwai inda zan iya kwatanta maki suna bada hayar daki a kusa da nan. Bayan makaranta gidan hayar yake. Amma naga kamar bai kamace ki bane dan naga alamun ks ustaziya ce. Gidan a hade yake maza da mata."

Basma tace, "gaya min ina ne zan iya zama, kowa da halinsa yake zama. Ni dai in samu hayar daki kusa da makaranta inda da kafafuwana zan iya shigowa ba sai na hau mota ba".

Malama Zainab tace, "To idan kika fita daga makarantar nan, ki mike dama, zuwa karshen bangon jami'ar nan zaki ga wani gida haka a saman kofar gate din an rubuta 'SHAGALA HOSTEL'. 

Basma ta dafe kirji tace, "Shagala kuma Malama?"

Malama tace, "shiyasa nace ai naga baza ki iya zama a wajen ba."

Basma tace, "a'a zan iya, suyi shagalar su ni karatu ya kawo ni. Nagode Malama."

Malama Zainab tace, "amma fa kiyi hanzarin zuwa, domin nasan yanda hostel din makarantar nan ya cika, duk mai son samun saukin karatu da zaman makaranta zai nufi wancan hostel din ne. Idan har ya cika to sai dai ki koma cikin gari, ki dinga tafiyar awa guda kullum in kina da lakca."


Basma na jin haka bata tsaya wata-wata ba, sai taja jakar kayanta a guje, ta nufi hanyar Shagala Hostel. 



••••••••••••••••••••••••

"Gaskiya ni in ba dubu sittin anka lalo min ba, bana sakin wanga daki, wanga daki shi kadai a ragowar dakunan gidan ga. Idan baka iya biyan kudinsa hakuri anka yi kawai. Masu kudi hannu suna tahe, in sun zanniya su cako min kudi in basu dan makulli." Manaja Tanimu ya fada fuska a daure, yana magana yana murza gashin baki. 

Musa yace, "Haba ranka shi dade, nifa dan makaranta ne, ka taimaka min ka karba dubu arba'in, yanzu haka in na baka dubu arba'in dinnan banda ko na abinci ma."

Manaja yace, "to wanga ar matsala ta? Ni kudi sunka matsala ta, can ka gane ma kanka. Lalo min naira in baka matsugunni."




Musa ya durkusa gwiwa biyu yana rokon Manaja ya taimaka masa ya ba shi hayar dakin nan guda daya da ya rage a Shagala Hostel, domin in bai samu dakin nan ba, bai san yanda zata kasance masa ba. Shi dai bai da kowa a garin nan, kuma bazai iya zuwa makaranta daga cikin gari ba kullum. 



Suna cikin drama Manaja ya dage sai rashin mutunci yake zubawa akan daki, sai ga Basma ta shigo gidan da kayan ta a sukuwane. Tana cin karo dasu tace, "Hayar daki nake so, akwai?"

Manaja ya washe baki tare da cewa, "to ka gani ko, ni ar dan sa'a, daki ko nawa nace a biya zanka samu mai karbe shi. Ke yarinya akwai daki daidai ke wallah, ince kina da kudi ko, dubu sittin kacal zaki biya ba tsada."

Basma tace, "ka taimaka min dubu talatin nake dashi."


Manaja dake washe baki yaga Basma yar bul-bul kamar wata hajiya sai ya turbune fuska. Ya juya mata keya tare da cewa, "a'a ke ma jaye gehe, mai dubu sittin zan ba daki."

Musa dake tsaye gefe har ya fidda rai da yaga Basma tazo, yayi zaton tana da isassun kudin karbar dakin ma. Sai ya fara murna da yaji kudinsa sun fi nata. Yayi saurin cewa, "Manaja ka taimaka min, kaga kudina sun fi nata yawa ma. Ka bani dakin nan ko bashi ne ka biyo ni zan cika maka."

Manaja yace, "Musa kake ko Mushe ne ma, bazan baka dakin ga ba hwa, ko in rantse maka da sirdin dokin Shehu Danhodio ne?"

Musa yace, "a'a kar ka rantse."

Manaja yace, "to da sai in rantse, dan babbar rantsuwa ce a guna, in tabbatar maka bazan bada dakin ga ba sai mai dubu sittin."


Basma fa hankalinta ya tashi, taji yanda Manaja ya shuka ma wanda ya fita kudi ma rashin mutunci, to ina ga ita. Ta rasa mafita, ita dai ta san rufin asirinta shine samun dakinnan. Ta kalla Musa ta dan langabe kai tare da cewa, "Malam tunda kai namiji ne ko zaka taimaka min da bashin dubu talatin daga cikin kudin ka, kai nasan ko wajen abokai zaka iya zama. Zan biya ka in na samu."


Ai sai Musa yaji kamar ta buga masa tabarya akai. Ya buga mata harara tare da cewa, "kar ki raina min hankali mana, magulmaciya kawai, ba nan kika ga zan karba daki ba, kinzo zaki dagula mana lissafi. Tunda baki da kudi ki kara gaba mana."

Sai fa Basma ta harzuka da taji zai gaya mata magana, "to kai kudin gare ka ne zaka nuna min gadara. To a baka dakin mana in kana da kudin muga."



Aisha wadda dakin ta ke kallon dakin da ake rigima akai, tana zaune a waje tana yanka kayan miya. Tace masu, "me zai hana ku hada kudi rabi da rabi ki kar ba dakin mana, ba sai ku zauna ku biyu ba."


Musa ya girgiza kai yace, "Subhanallah! Duk inda namiji ya zauna da mace ai shedan na wajen, balle kuma ace dakin kwana. Inaaa! Haramun bazan iya ba."

Basma tayi murmushi tare da kallon Aisha tace, "ke kuwa yar uwa, me zai hada ni zama daki daya da Qato, ai ko zaman gidan dan ya zama dole ne. Auzubillah, ba dani ba..............


To mu dai yan kallo ne, muga tsiyar ustazancin nasu, aje a dawo dai dole aba bura da duri abinci. 


Nectar Boy

Cikakken littafin yana Okadabooks application na wayar android.

Domin samun labarai daga Taskar Nectar Boy sai ku hau website dina ta hanyar danna blue rubutun nan na kasa:

nectarboyblog.blogspot.com

Domin karin bayani akan Okadabooks ana iya tuntuba na ta whatsapp @ 08169067723

BANA TURA LABARI A WHATSAPP
BANA SA MUTANE A GROUP
BANA HADA ALAKA TSAKANIN MUTANE
BAYANIN OKADABOOKS KAWAI NAKE

Comments

Zafaffan Labarun Nectar Boy

YAR TALLA COMPLETE

FADILA DA FATI

MAKARANTAR BODIN 1

SALE DA YANMATA HUDU

YAN MADIGO

KWARTO

,CIN BABA NA

A GIRGIZA KWANKWASO 4

KWARTAYEN ALHAJI

LIDIYA ƳAR MAGUZAWA