MUTUM KO ALJAN
MUTUM KO ALJAN •••••••••••••••••••••• Doguwa ce sosai, tsayinta ya kai na maza da yawa. Fuskar mai tsayi ce kamar ta fulani. Idanuwanta kuwa farare ne kal-kal gwanin sha'awa, tamkar an narka ruwan zinari cikin ruwan idon. Hanci dan siriri kamar murfin biro, sannan ga wasu yan manyan lebba masu taushin kallo. Wuyanta dogo ne mara fadi, tana a tsaye kamar mai gantsaro kirji, amma ba hakan bane. Tudun nononta ne yake bayyana hakan, a tsaitsaye nonuwan suke, sun dago rigarta gwanin ban sha'awa. Doguwar rigar dake jikinta ta matse ta sosai, don haka shaf din kugunta ya bayyana. Kamar kwalbar lemon coca-cola. Kwankwason nan mai fadi ne sosai, hakazalika cinyoyinta suke da kauri, ga wasu yan siraran dogayen kafafu da take dasu. Kamshin turarenta ya fara bugun hancina, kafin sanyayyar muryarta ta doki dodn kunne na, wanda hakan ya dawo dani daga dimaucewa. "Aminci ya tabbata a gare ka", ta fada cikin sauti mai dadi. "Amin, kuma kema aminci ya tabbata a gare ki zinar