Posts

Showing posts from November 19, 2017

DAN AUTAN HAJIYA

Image
DAN AUTAN HAJIYA •••••••••••••••••• Tun bayan auren Tanko da Lami, Sallau da Idi basu taba zuwa gidan su ba. Sai dai in an hadu a hanya a gaisa sama sama, ana yi ana jin haushin juna. Babu abunda ke zuciyar Sallau dan autan hajiya irin ya dakusar da Tanko.  Watarana suna zaune da Idi ana shan rake, sai Sallau yace, "Wai yanzu Idi haka zamu zuba ido a garin nan, Tanko yaci amanar mu kuma ya zauna lafiya?" Idi yace, "kamar ka shiga zuciya na Sallau, nima maganar dake raina kenan, kuma har na zo da wata yar shawara." Sallau yace, "ina jin ka, meye shawarar?" Idi yace, "kasan lokacin da aka masa auren nan, an ba shi wata tunkiya mai ciki, yanzu haka ta kusa haihuwa. To abunda Tanko ya mallaka kenan, daga gonar ubansa sai wannan tunkiyar. Ni a ganina idan muna so ya dawo hanyar mu, sai mun talauta shi, sannan zai dawo gidan jiya da ya bar mu." Sallau yace, "kuma fa ka kawo shawara, wato mu sace tunkiyar