MUTUM KO ALJAN
MUTUM KO ALJAN ••••••••••••••• Tun daga nesa na hangota, tana tafiya a hankali cikin kasaita da rangwada kamar bata son taka kasa. Tafiyar ma kadai abun kallo ce. A hankali ta tunkaro inda nake zaune. A lokacin da naga fuskarta, sannan na kara kallon surar jikinta sai naji hankalina ya tashi. Na bude baki a rude ina kallonta. Doguwa ce sosai, tsayinta ya kai na maza da yawa. Fuskar mai tsayi ce kamar ta fulani. Idanuwanta kuwa farare ne kal-kal gwanin sha'awa, tamkar an narka ruwan zinari cikin idon. Hanci dan siriri kamar murfin biro, sannan ga wasu yan manyan lebba masu taushin kallo. Wuyanta dogo ne mara fadi, tana a tsaye kamar mai gantsaro kirji, amma ba hakan bane. Tudun nononta ne yake bayyana hakan, a tsaitsaye nonuwan suke, sun dago rigarta gwanin ban sha'awa. Doguwar rigar dake jikinta ta matse ta sosai, don haka shaf din kugunta ya bayyana. Kamar kwalbar lemon coca-cola. Kwankwason nan mai fadi ne sosai, hakazalika cinyoyinta suke da kauri, ga wasu yan siraran d...