KWARTAYEN ALHAJI 2
KWARTAYEN ALHAJI 2 •••••••••••• Yana zuwa dakin Halima yasa kai zai shiga da sauri sai yaji, 'GWARAM!' Sai ga wasu yan kananan taurari suna juyawa a kan sa. Ya farfado da kyar domin ganin menene, ashe Halima ta rufe kofar dakinta bai sani ba, shine yana tura kai yayi gware da kofar karfen nan na dakin. Alhaji ya shafa goshinsa yaji har wani dan kulu ya fito masa. Ya kwankwasa kofar dakin yana kiran sunan Halima, tayi banza dashi kamar bata ji ba. Ashe dama mamayarta yayi ya shigo dazun nan. Yana fita kuwa ta rufe dakinta, dan yanzu ita a cewar ta, ta zama yar madigo babu ruwan ta da namiji. Duk magiyar Alhaji amma Halima bata bude kofa ba, har alkawarin kujerar makka yayi mata domin ta bude masa kofa, tayi biris dashi taqi budewa. Da ya gaji da magiya, sai ya aje mata tabaryar ta ya nufi dakin Asiya domin yaga ko zata ba shi yaci durin da yaqi ci jiya. Yana zuwa ya kwankwasa kofar dakin. Asiya yace, "Waye?" Yace, "Maigidan ne!" ...