JAURO YAGA GATO Jauro ya kalli Mado da Ado yace, "to tunda kunshe haka, na yarda. Amma ni ban taba shi ba, yanzu ina so inshi inji yanda ake ji, ya za ayi?" Mado yace, "bari muje wajen Lamunde, dama in ina son shin gutsu wajen ta nake zuwa da naira hamsin dina, in ta fito tallan nono sai mu shiga gona". Ado yace, "haba kaima kana shin Lamunde dama? Nima ai ita nashi dazu da nazo ina ba Jauro labarin nashi gutsu". Mado da Ado suna cikin labarin yanda dandanon gutsun Lamunde yake, shi kuma Jauro na gefe haushi ya cika shi, wai shi suke so su maida wawa. Har wani kirkiro labarin gutsun Lamunde ake, basu san duk ya gano karya suke ba. Cikin haka kawai sai ya hango Lamunde tafe kan hanya, dauke da kwaryar nononta na saidawa. Tana gantsare kirji nononta na tsalle. Jauro yayi tsalle sama, ya kwarara ihu, yace "yau za a kure mai karya aradu. Ga Lamunde can tazo, sai an nuna min yanda ake shin gutsu yau". Mado da Ado suka hango Lamunde, ita ma ta ...