BAGIDAJIYA
BAGIDAJIYA ••••••••••••••••• ••••••••••••••••• Alhaji Sani na zaune a falonsa ya bata rai, idanuwansa sun yi jawur cikin bacin rai. Yana zaune yana duba agogo, zuwa wani dan lokaci sai ya tashi ya leka taga. Sannan ya kara duba agogo yana kwafa. Can sai yaji an bude gate, sannan yaji shigowar motar Faisal. Ya tsaya ta taga yana kallon Faisal cikin takaici. Bayan Faisal ya rufe motarsa, ya shigo gidan kai tsaye. Yana turo kofar falon sai Alhaji Sani ya chakumo kwalar rigarsa. Yaja sa har cikin daki kamar rago. Suna shiga dakin Alhaji ya cire babbar rigarsa, ya dauko dorina. Idanuwan Faisal suka fito tsuru-tsuru, babu hanyar fita ga bulala yana kallo. Alhaji ya fara lafta ma Faisal dorinar nan a tsakar baya. Faisal na ihu, “Wayyyoo Baba, wayyyo kayi hakuri, na shiga uku, wayyyo...